Majalisar dattawa ta dage zaman ta na tsawo makonni 2

Majalisar dattawa ta dage zaman ta na tsawo makonni 2

- Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa nan da makonni biyu domin ba yan majalisar damar mayar da hankali ga lamuran tattarin arziki

- Hakan ya biyo bayan roko da shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan yayi

- Majalisar za ta dawo zama ne a ranar 2 ga watan Afrilu

Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa nan da makonni biyu domin ba yan majalisar damar mayar da hankali ga lamuran tattarin arziki.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Ahmed Lawan ne ya gabatar da batun dage zaman a ranar Laraba, 20 ga watan Maris.

Majalisar dattawa ta dage zaman ta na tsawo makonni 2
Majalisar dattawa ta dage zaman ta na tsawo makonni 2
Asali: UGC

Mista Lawan (APC, Yobe ta Arewa) ya yi roko ga yan majalisar da su dge zamansu har zuwa ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Sanatocin sun amince da rokon bayan tattaunawa a tsakaninsu.

A ranar Talata, 19 ga watan Maris ne kasafin kudin ya isa zagaye na biyu a majalisar dattawan.,

Bayan gabatar da kasafin kudin, sai majalisar ta bukaci kwamitinta akan kasafin ta yi aiki kan kasafin naira triliyan 8.8.

KU KARANTA KUMA: Da dumin sa: PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za su yanke hukunci akan yadda za a raba mukaman majalisar dokokin kasar a mako mai zuwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Biyo bayan zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, APC ta samu mafi rinjayen kujeru a majalisun biyu na tarayyar kasar, don haka hana sanya ran ita za ta kafa shugabanci.

Majiyoyi a Abuja sun bayyana cewa jam’iyyar za ta samu matsaya a kowani lokaci fara daga ranar Talata mai zuwa kan matsayin da kowani yanki zai samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel