PDP ta yi watsi da umarnin kotu a kan sakamakon zaben gwamnan Bauchi

PDP ta yi watsi da umarnin kotu a kan sakamakon zaben gwamnan Bauchi

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana kin amincewar ta ka abinda ta kira amfani da fanin shari'a da kotu da jam'iyyar APC tayi na dakatar da tattaa sakamakon zaben gwamna a Bauchi duk da cewa an kammala kidiya kuri'un kuma PDP ce tayi nasara.

Jam'iyyar ta PDP ta ce wannan matakin da APC dauka ya yi kama da abinda ya faru na zaben 1993 inda ta yi ikirarin jam'iyyar na APC da wasu balagurbi cikin INEC ke kokarin tayar da rikici da gurgunta demokradiyar mu.

Wannan na dauke ne cikin wata sako da sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar 20 ga watan Maris ta shafin Facebook na jam'iyyar.

PDP ta yi watsi da hukuncin da aka yanke na dakatar da zaben Bauchi
PDP ta yi watsi da hukuncin da aka yanke na dakatar da zaben Bauchi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: PDP tayi karar Justice Inyang Ekwo saboda dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi

"INEC kadai ke da ikon kidiya kuri'u, dakatar da kidiyar ko kuma cigaba da kidiya kuri'un kamar yadda aka gani a Bauchi. Muddin ba a gama kidaiya kuri'u an sanar da sakamakon zabe ba, ba bu wanda doka ta bawa iko ya yiwa INEC katsalandan," inji shi

PDP tayi gargadin cewa muddin aka bari jam'iyyar APC ta cigaba da yin katsalandan cikin harkokin zabe tabbas demokradiyar mu za ta shiga cikin hatsari kuma zamu tsinci kan mu cikin halin tabarbarewar doka da oda.

Ya cigaba da cewa "Sashi na 87(10) na dokar zabe ya bayyana a fili cewa kotu ba ta da ikon zartar da wani hukunci ko bayar da umurni na dakatar da zaben cikin gida ko babban zabe da sauran harkokin zaben.

"Da wannan ne muke ke kira ga INEC ta tabbatar da cewa tana aikinta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada."

PDP ta kuma yi kira ga fannin shari'a ta cigaba da gudanar da aikinta ba tare da bari jam'iyyar APC tana neman jefa ta cikin matsalolin da ka iya lalata mana demokradiyar mu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel