Karin albashi: Kungiyar Kwadago ba za ta amince da karin haraji ba - Ajaero

Karin albashi: Kungiyar Kwadago ba za ta amince da karin haraji ba - Ajaero

Joe Ajaero, shugaban hadadiyar kungiyar kwadago, United Labour Congress, ULC, ya ce ba za su amince da kari a kan harajin kayayakin masarufi, VAT, da gwamnatin tarayya ke neman yi domin biyan sabon albashi mafi karanci.

Mr Ajaero ya yi wannan furucin a hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN a Legas yayinda ya ke mayar da martani a kan zancen da gwamnati tayi na neman izinin kara harajin kayan masarufi, VAT domin samun kudin biyan sabon albashi mafi karanci na N30,000.

A ranar Talata ne Majalisar Tarayya ta amince da N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci na ma'aikatan kasar watanni biyu bayan Majalisar Dokoki na Tarayya ya amince da karin albashin.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta saka sharadin biyan sabon albashi na N30,000

Karin albashi: Kungiyar Kwadago ba za ta amince da karin haraji ba - Ajaero
Karin albashi: Kungiyar Kwadago ba za ta amince da karin haraji ba - Ajaero
Asali: Twitter

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Sanata Udo Udoma ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta kara harajin kayayakin masarufi, VAT da 50% kafin karshen shekarar 2019 domin ta samu daman biyan sabon albashin.

A halin yanzu dai 5% 'yan kasuwa da kamfanoni da ke biya a matsayin harajin na VAT.

Shugaban na ULC ya ce babu wata yarjejeniyar cewar za a kara haraji bayan anyi karin albashi a lokacin da suka zaman tattaunawa game da karin albashin.

Ya ce idan da gwamnatin tana ganin za tayi amfani da harajin VAT din ne wurin cike gibin karin albashin da za tayi, ya dace da an tattauna a kan lamarin tare da masu ruwa da tsaki.

"Ba a sanar da mu wani sharadi na musamman ba yayin tattaunawar da mu kayi na karin albashi, idan da akwai batun karin harajin VAT, da masu ruwa da tsaki sun tattauna a akai," inji shugban kwadigon.

Ya yabawa majalisar dattawa kan amincewa da kudirin karin albashin cikin gaggawa ya kuma bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ratabba hannu a akan kudirin domin a zartar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel