Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun far ma wasu masallata a hanyarsu ta zuwa masallaci a Osogbo

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun far ma wasu masallata a hanyarsu ta zuwa masallaci a Osogbo

- Wasu yan bindiga sun far ma wasu masallata a unguwar Aleluya da ke Osogbo, babbar birnin jihar Osun a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa masallaci da asuba

- Yan sanda sun yi nasarar cafke mutum guda daga cikin yan bindigar a lokacin da suka kai agaji bayan samun labarin lamarin

- Kakakin yan sandan Osun, Folasade Odoro ta tabbatar da afkuwar lamarin

Musulmai a unguwar Aleluya da ke Osogbo, babbar birnin jihar Osun sun sha da kyar yayinda wasu yan bindiga suka far masu da safen nan a hanyarsu ta zuwa masallaci.

Musulmai a yankin sun bayyana cewa wasu mutane dauke da bindigogi sun far masu sannan suka yi kokarin bude masu wuta a hanyarsu ta zuwa masallaci domin sallatar Subuhi.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun far ma wasu masallata a hanyarsu ta zuwa masallaci a Osogbo
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun far ma wasu masallata a hanyarsu ta zuwa masallaci a Osogbo
Asali: Depositphotos

Daya daga cikin wadanda abun ya cika da su da ya kira yan uwansa domin neman agaji, ya bayyana cewa yan uwansa ma sun fuskanci makamancin haka.

Mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar, Mista Abu Mustapha wanda ya ji labarin afkuwar lamarin ya tura yan sanda daga yankin Dada Estate.

KU KARANTA KUMA: APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa

Yan sandan sun isa wajen akan lokaci sannan sun kama daya daga cikin yan bindigan sun kuma kwato bindiga a hannunsa.

Kakakin yan sandan Osun, Folasade Odoro ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel