A daren yau za mu kawar da kungiyar ISIS - Trump

A daren yau za mu kawar da kungiyar ISIS - Trump

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump, ya ce a ranar Alhamis ta yau, 21, ga watan Maris, za a kawo karshen babbar kungiya mafi munin ta'adda ta duniya mai lakabin ISIS, Islamic States of Iraq and Syria.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Mista Trump ya ce a yau dinnan ta Alhamis, 21 ga watan Maris, za a kawar da kungiyar ISIS daga daular ta ta karshe da ke kasar Syria.

Mai rike da akalar jagorancin dukkanin kasashen duniya ya bayyana hakan cikin fadar sa ta White House. Trump ya ce a halin yanzu daular karshe ta kungiyar ISIS da ke kasar Syria tamkar a tafin hannun rundunar dakarun sojin kasar Amurka ta ke kuma a yau Alhamis za su a ga bayanta.

Donald Trump
Donald Trump
Asali: UGC

Shugaban na kasar Amurka ya ce gabanin faduwar ranar yau ta Alhamis, 21 ga wata, kungiyar ISIS za ta zamto tarihi duba da yadda ta ci Karen ta ba bu babbaka a lokutan baya musamman cikin shekaru biyu da suka gabata.

KARANTA KUMA: Harin Makiyaya ya salwantar da rayuka 10 a jihar Benuwe

A baya can kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, kasar Amurka ta yi ikirarin cewa kingiyar ISIS ita ce barazana mafi muni da kuma hadari da taba fuskanta. Amurka ta sha alwashi na wajabtawa kanta murkushe kungiyar a kasar Iraqi da kuma Syria.

Amurkan ta ce hare haren da take kai wa mayakan kungiyar ta sama sun taimaka wajen rage karsashinta, amma kuma akwai bukatar samar da wata runduna ta soji ta hadaka domin gamawa da kungiyar baki daya.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, ya bayyana kungiyar a matsayin, wadda take da kwarewa da kuma samun kudade sosai, fiye da duk wata da Amurka ta gani a baya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel