Zaben Najeriya abun kunya ne a idon duniya - Amurka

Zaben Najeriya abun kunya ne a idon duniya - Amurka

Tsohon Jakadan Amurka zuwa Najeriya, John Campbell, ya fedewa shugaban kasa Muhammadu Buhari Biri har wutsiya dangane da yadda ta kaya a babban zaben kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Mista Campbell ya yi kaca da shugaban kasa Buhari da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, dangane da yadda su ka fifita bukatun su na kawuna sama da kishin kasa da kuma al'ummar Najeriya.

Zaben Najeriya abun kunya ne a idon duniya - Amurka
Zaben Najeriya abun kunya ne a idon duniya - Amurka
Asali: UGC

Tsohon Jakadan ya ce, jam'iyyar APC da kuma PDP da suka kasance manyan jam'iyyu biyu na kasar nan sun kauracewa duk wata manufa da akidu na dimokuradiyya da a halin yanzu sun sanya siyasa tsagwaran ta a gaban su a madadin shimfida tsare-tsaren na ci gaban kasa.

Campbell cikin wani rubutu da ya wallafa mai lakabin yadda zaben Najeriya ya zamto abun kunya a idon duniya, ya yi ikirarin da cewa rzaben cike ya ke da sahihan zargi na magudi gami da yadda mafi akasarin al'umma su ka kauracewa zaben ta fuskar rashin kada kuri'u.

Yayin ci gaba da farkewa Atiku da shugaba Buhari Laya, Mista Campbell ya hikaito yadda kowanen su ya gudanar da yakin neman zabe ba tare da kulawa da wasu muhimman ababe da kasar nan ke matsanancin muradi wajen fidda A'i daga Rogo.

Atiku da Buhari sun nuna halin ko in kula yayin yakin zaben su inda Mista Campbell yayin wassafa jerin muhimman ababe da Najeriya ke muradi domin riskar tudun tsira sun hadar da samar da tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da ta'addancin Boko Haram ya yi kamari.

KARANTA KUMA: Ba bu lallai Atiku ya cimma nasara wajen kalubalantar sakamakon zabe - Tsohon Jakadan Amurka

Sauran muhimman ababe da jiga-jigan biyu suka kauracewa fayyace yadda za su kawo karshen su kamar yadda tsohon tsohon jakadan ya zayyana sun hadar da rikicin kabilanci da addini, takaddamar rabe-rabe arzikin man fetur a yankin Neja Delta, sauyin yanayi da kuma kalubale na yawaitar adadin al'ummar kasar nan.

Ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda zaben bana ya gudana cikin nakasu ka ma daga dage zaben zuwa tsawon mako guda, rashin bai wa Matasa damar shiga harkokin siyasa a sakamakon yadda dattawa su ka rike makogoron Talakawa da kuma yadda shaidu gami hujjoji su ka tabbatar da yadda aka haramtawa al'umma zabe a wasu yankunan kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel