Ba bu lallai Atiku ya cimma nasara wajen kalubalantar sakamakon zabe - Tsohon Jakadan Amurka

Ba bu lallai Atiku ya cimma nasara wajen kalubalantar sakamakon zabe - Tsohon Jakadan Amurka

Tsohon Jakadan kasar Amurka zuwa Najeriya, John Campbell, ya ce, ba bu lallai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya cimma nasara wajen kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Mista Campbell ya ce duba da yadda al'amurra ke ci gaba da gudana a kasar nan ta Najeriya da su ka sabawa tsari na dimokuradiyya, ba bu lallai Atiki ya cimma nasara yayin kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa a gaban Kotu.

Atiku tare da tsohon Jakadan Amurka; Campbell
Atiku tare da tsohon Jakadan Amurka; Campbell
Asali: Facebook

Kasancewar gagarumar tazara ta yawan kuri'u kimanin miliyan hudu da ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin zaben kasa, ba bu lallai Atiku ya samu nasara a gaban Kotun wajen kalubalantar sakamakon zaben kamar yadda tsohon Jakadan ya raja'a a kai.

Kazalika Mista Campbell cikin zayyana dalilan sa ya ce, ba ya ga kin bayyana rashin aminci, al'ummar Najeriya sun karbi sakamakon zaben hannu biyu-biyu ta hanyar rungumar makomar su ta shugabanci da ta kasance a karkashin shugaban kasa Buhari.

Mista Campbell ya kara da cewa, rashin fitowar babban kaso wajen kada kuri'a yayin babban zabe, na haskaka yadda a halin yanzu al'ummar Najeriya su ka fidda rai da tsarin dimokuradiyyar kasar nan tare cewar ba ta da muhalli a cikin ta.

KARANTA KUMA: Nasabar Buhari ta hana rushewar jam'iyyar APC, ta rike ta kyam - Ministan Neja Delta

Jaridar Legit.ng cikin wani rahoton mai nasaba da wannan ta ruwaito cewa, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben inda a halin yanzu ya gabatar da wasu korafe-korafe biyar a gaban Kuliya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel