Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi

Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi

Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a garin Abuja, a yau Laraba ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar zuwa gobe Alhamis biyo bayan takaddamar umarnin da ta shimfida na haramta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Biyo bayan umarnin haramtawa hukumar zabe ta kasa ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, babbar kotun tarayya bisa jagorancin Mai shari'a Inang Ekwo, ta dage sauraron karar da ta fara a yau Laraba zuwa gobe Alhamis.

Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi
Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi
Asali: Depositphotos

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, babbar kotun ta dage sauraron karar a sanadiyar rashin samun isasshen lokaci na gabatar da shaidu daga bangaren hukumar INEC mai kalubalantar hukuncin da kotun ta zartar.

Ba ya ga hukumar zabe ta kasa, sauran wadanda takaddamar hukuncin kotun ya shafa gami da ruwa da tsaki cikin shari'ar sun hadar da gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abubakar da kuma jam'iyyar sa ta APC.

KARANTA KUMA: Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam

A ranarTalata jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana takaicin ta dangane da hukuncin da babbar kotun tarayya ta zartar na gindaya umarnin haramtawa hukumar zabe ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan kaddamar da hukuncin zaben gwamnan jihar bai kammala ba, hukumar zabe ta yi amai ta lashe abin ta wajen yanke hukuncin ci gaba da tattara sakamakon zaben tare da cewar ba bu wani dalili na maimaicin sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel