Nasabar Buhari ta hana rushewar jam'iyyar APC, ta rike ta kyam - Ministan Neja Delta

Nasabar Buhari ta hana rushewar jam'iyyar APC, ta rike ta kyam - Ministan Neja Delta

Ministan kula da harkokin yankin Neja Delta, Usani Uguru Usani, ya bayyana takaicin sa gami da damuwa ta hanyar babbatu dangane da yadda al'amurra ke ci gaba da gudana a jam'iyyar su ta APC mai ci a kasar nan.

Ministan Usani cikin kalami nasa, ya bayyana yadda nasabar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zamto wani babban tubali kuma kasurgumin ginshiki da ya hana rushewar jam'iyyar APC a kasar nan tare da rikon ta kyam ba bu ko girgiza.

Nasabar Buhari ta hana rushewar jam'iyyar APC, ta rike ta kyam - Ministan Neja Delta
Nasabar Buhari ta hana rushewar jam'iyyar APC, ta rike ta kyam - Ministan Neja Delta
Asali: Twitter

Ya ce kasancewar shugaban kasa Buhari a jam'iyyar APC ya hana rushewa tare da tabbatuwar martabar ta sabanin yadda aka kauracewa tafarki da kuma manufofi na akidu da su ka sanya aka assasa ta tun fil azal.

Ministan ya bayyana hakan a ranar Talata cikin garin Abuja yayin bayyana ra'ayin sa dangane da yadda ake tuhumar Ntufam Hilliard Eta, mataimakin shugaban jam'iyyar reshen Kudu maso Kudancin kasar nan da laifin sabawa akidu da ya sanya shugabancin jam'iyyar ya dauki hukunci na dakatar da shi.

Cikin makamanciyar takaddamar da ta sanya Ministan ya ke ci gaba da bayyana damuwa, Mista Hilliard ya hau kujerar naki ta rashin amincewa da tuhumar da ake ma sa tare da da cewa har ila yau ya kasance cikakken mamba na jam'iyyar mai tattare da lasisi.

KARANTA KUMA: Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mun samu cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta kirayi wani taron gaggawa na jiga-jigan ta bisa jagorancin shugaban ta, Prince Uche Secondus domin tattauna batutuwan siyasa musamman takaddamar zaben gwamnan jihar Ribas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel