APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa

APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa

Shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za su yanke hukunci akan yadda za a raba mukaman majalisar dokokin kasar a mako mai zuwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Biyo bayan zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da ya gufdana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, APC ta samu mafi rinjayen kujeru a majalisun biyu na tarayyar kasar, don haka hana sanya ran ita za ta kafa shugabanci.

Majiyoyi a Abuja sun bayyana cewa jam’iyyar za ta samu matsaya a kowani lokaci fara daga ranar Talata mai zuwa kan matsayin da kowani yanki zai samu.

APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa
APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa
Asali: UGC

Manyan matsayi hudu da za yi rabo tsakanin yankuna sune Shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, mataimakin Shugaban majalisar dattawa da mataimakin kakakin majalisar wakilai.

KU KARANTA KUMA: Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)

Wata majiya ta bayyana cewa ba don rashin kamala zabe a jihohin Benue, Sokoto, Adamawa, Plateau, Kano da Bauchi bad a APC ta dade da yanke hukunci.

Tuni dai wasu zababbun sanatoci da yan majalisa suka nuna ra’ayinsu na son mukaman, koda dai wasu sunce za su duk hukuncin da majalisa ta yanke.

Daga cikin masu neman kujerar Shugaban majalisar dattawa sun hada da Shugaban masu rinjaye a majalisa Ahmad Lawan (Yobe), Mohammed Ali Ndume (Borno), Danjuma Goje (Gombe) da kuma Abdullahi Adamu (Nasarawa).

An tattaro cewa Orji Uzor Kalu (Abia) da Benjamin Uwajumogu (Imo) ma sun nuna ra’ayinsu akan kujerar Shugaban majalisar dattawan.

A majalisar wakilai kuma sun hada da Shugaban masu rinjaye Femi Gbajabiamila (Lagos), Ahmed Idris Wase (Plateau), Mohammed Tahir Monguno (Borno), Abdulrazak Namdas (Adamawa), Aminu Suleiman (Kano), Babangida Ibrahim (Katsina) da kuma Umar Bago (Niger).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel