Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)

Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)

Gwamnatin jihar Kano karakashin jagorancin, Dr Abdullahi Umar Ganduje na nan tana gudanar da ayyukan ci gaba a yankin garin Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar.

A yanzu haka gwamnati ta fara aikin gina fanfon burtsatse guda 11 a wannan yanki na gama domin shawo kan wannan matsala ta karancin ruwa.

Baya ga fanfon burtsatse akwai kuma aikin hanya da aka fara a baya, wanda shi ma gwamnati take kammalawa.

Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)
Aikin gyara hanya da ke gudana a garin Gama, jihar Kano
Asali: UGC

Sannan kuma ana ta gyare-gyare a cibiyar lafiya ta Isah Kaita duk a yankin Gama.

Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)
Dakunan asibiti da ake gyarawa
Asali: UGC

A yankin Gama ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya sake zabe kafin tabbatar da wanda ya lashe zaben gwamna a jihar ta Kano. INEC dai ta shirya yin zaben ne a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama (hotuna)
Ana gab da sake zaben Kano, Gwamna Ganduje na nan na zuba ayyukan ci gaba a Gama
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Zaben Kano zagaye na 2: Ku guji 'yan takara masu dabi'ar Jaki, Kare ko Kaza - Sheikh Kalil

Wannan ayyukan ci gaba da gwamnatin ke yi a yankin na gama ya haifar da cece-kuce inda jama’a da dama ke tunanin ko gwamnan nayi ne don ya samu kuri’un jama’ar yankin a lokacin zaben da za a sake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel