Gwamna Bello na shirin baza yan daba a Benue don yin magudin zabe – Matasa sun yi zargi

Gwamna Bello na shirin baza yan daba a Benue don yin magudin zabe – Matasa sun yi zargi

Shugabannin kungiyar matasan jihar Benue, sun koka kan zargin cewa akwai wani kulli da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ke yi domin baza yan iska a jihar a lokacin zaben da za a sake yi mai zuwa a ranar Asabar, 23 ga watan Maris domin yin magudi a sakamakon zaben.

Matasan sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saita gwamnan na jihar Kogi inda suka yi gargadin cewa idan har aka aiwatar da munakisan toh babban rikici zai barke a jihar.

Shugaban kungiyar, Kwarad Terrence Kuanum, wanda yayi gargadin a jiya Talata, 19 ga watan Maris a Makurdi yayi zargin cewa an hada kai ne da wasu gwamnonin arewacin kasar domin shirya wannan tuggun.

Gwamna Bello na shirin baza yan daba a Benue don yin magudin zabe – Matasa sun yi zargi
Gwamna Bello na shirin baza yan daba a Benue don yin magudin zabe – Matasa sun yi zargi
Asali: UGC

Da yake martani akan lamarin, babban sakataren labaran gwamnan jihar Kogi, Mista Muhammed Onogu yace: “Zargin duk kanzon kurege ne da kuma makirci. Mutanen Benue su fuskanci zabensu sannan su yi abunda suke ganin zai fisshe su.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai tafi Umrah ba, a yanzu haka yana jagorantar zaman majalisar zartarwa

“Gwamnan jihar Kogi na da sabgar gabansa a jiharsa. Ban san daga ina suka samu labarinsu ba amma abunda na sani duk karya ne sannan muna bukatar jama’a da su yi watsi da irin wannan kagaggen labarin."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel