Buhari bai tafi Umrah ba, a yanzu haka yana jagorantar zaman majalisar zartarwa

Buhari bai tafi Umrah ba, a yanzu haka yana jagorantar zaman majalisar zartarwa

Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa, Abuja. Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake rade-radin cewa shugaban kasar ya tafi kasa mai tsaki don yin aikin Umrah.

Hazalika, mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ma ya halarci zaman. An tattaro cewa an fara zaman ne a lokacin da Shugaban kasar ya isa zauren majalisar da misalin karfe 10:59am.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Munguno da kuma ministoci 23 duk sun hallara a taron.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu rahotanni suka bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya, kasa mai tsarki don gudanar da Ibadan aikin Umrah, kuma tuni ya mika ragamar kula da Najeriya a hannun mataimakinsa Yemi Osinbajo.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje

Wadannan rahotanni sun karade shafukan sadarwar zamani, musamman na Facebook da na Twitter, sai dai yayin da wasu rahotanni suke nuni da cewa a yammacin Talata ne Buharin ya wuce, wasu rahotannin kuma cewa suka yi a yau Laraba ne zai wuce.

Sai dai manya manyan hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari basu tabbatar da hakan ba, kuma basu bayyana hakan a shafukansu na sadarwar zamani ba, daga cikin hadiman da Legit.ng ta bibiya akwai Garba Shehu da Femi Adesina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel