Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam

Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam

A yayin da tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya kasance daya daga cikin malamai ma su horar da dalibai a jami'arNOUN (National Open University) reshen ta na jihar Ogun, a jiya Talata an bayyana albashin da ya ke samu a kowace shekara.

Za ku ji cewa kasancewar sa malami mai karantaswa a jami'ar Najeriya ta NOUN, tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya na daukar albashi na Naira dubu arba'in a kowace shekara.

Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam
Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam
Asali: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban jami'ar, Farfesa Abdallah Adamu, shi ne ya bayyana hakan a jiya Talata.

Shugaban jami'ar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya bayar da tabbacin yadda a halin yanzu tsohon shugaban kasa ke kulawa tare da horas da wasu dalibai biyu a fannin nazarin Tauhidin addinin Kirista da ya kasance mai digirin digirgir a fannin.

KARANTA KUMA: Shugaban kasar Koriya ta Kudu ya taya shugaba Buhari murnar samun nasarar tazarce

Ganawar shugaban jami'ar ta gudana ne domin bayyana shirin bikin yaye dalibai kimanin 20,799 da za a gudanar a kwana kwanan nan.

Farfesa Adamu ya bayyana yadda jami'ar NOUN ta dauki Obasanjo aiki a shekarar 2018 da ta gabata tare da tanadin ofis a birnin Abeokita inda a halin yanzu ya ke daukar albashi na Naira 40,000 a kowace shekara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel