An fasa bututun mai 257 a cikin wata guda kacal - NNPC

An fasa bututun mai 257 a cikin wata guda kacal - NNPC

Bayanai daga rahoton kudi da ayyuka na kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC) ya nuna cewa an fasa bututun mai 257 mallakar kamfanin a cikin watan Disamban 2018.

Hakan ya sa an samu hauhawa daga bututu 60 da aka fasa daga watan Nuwamba da kusan 197.

Adadin barnar da aka samu a watan Disamba ya fi na bututun man fetur 219 da aka shigo da shi daga watan Oktoban 2018.

Daga cikin butun guda 257, daya yaki gyaruwa sannan shida sun tsatsage.

An fasa bututun mai 257 a cikin wata guda kacal - NNPC
An fasa bututun mai 257 a cikin wata guda kacal - NNPC
Asali: Twitter

A bisa ga rahoton da aka wallafa a shafin yanar gizon kamfanin a ranar Talata, 19 ga watan Maris bututun mai shida sun gaza gyaruwa sannan biyu sun tsatsage daga cikin 197 da aka lalata a watan Nuwamba.

Tashoshin da aka fi samun yawan fashe-fashen sune Ibadan-Ilorin- 90, Mosimi-Ibadan- 69 da kuma Atlas Cove-Mosimi network- 57. Wadannan tashoshin ne ked a kaso 34 cikin 100 na matsalar.

A bisa ga rahoton watan Disamba, kasuwar man fetur na kamfanin wato Petroleum Product Marketing Company (PPMC), ta siyar da lita biliyan 1.96 na fetur.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje

Hakan na nufin an samu Karin bukata a watan Disamba, yayinda kamfanin ta siyar da lita biliyan 1.09 a watan Nuwamban 2018.

A watan Disamba, kamfanin ta samar da mafi yawan kayayyakin bukata, inda ta isar da lita biliyan 1.94. kimanin lita miliyan bakwai na kalanzir da kuma lita miliyan 140 na man diesel aka siyar a watan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel