Zaben shugaban kasa 2015: Jonathan ne ya kashe kansa na kin zuwa kotu - Buba Galadima

Zaben shugaban kasa 2015: Jonathan ne ya kashe kansa na kin zuwa kotu - Buba Galadima

- Buba Galadima, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yiwa kansa sakiyar da ba ruwa da ya ki zuwa kotu bayan kammala zaben 2015

- Buba Galadima ya bayyana cewa zuwa kotu bayan kammala zabe ba wani bakon lamari bane, kasancewar shi ma shugaba Buhari ya sha kuwa kotu tun 2003

- Idan ba a manta ba, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa PDP da Atiku sun maka shugaban kasa Buhari kotu kan kalubalantar sakamakon jarabawar WAEC dinsa

Buba Galadima, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Atiku Abubakar a zaben 2019 da ya gabata, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yiwa kansa sakiyar da ba ruwa da ya ki zuwa kotu bayan kammala zaben 2015.

Buba Galadima ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da gidan talabijin na Channels Tv, yana mai cewa zuwa kotu bayan kammala zaben shugaban kasa ba wani bakon lamari bane, kasancewar shi ma shugaban kasa Buhari ya sha kuwa kotu tun daga zaben 2003.

Da ya ke tsokaci kan yadda jama'a ke ganin laifin Atiku Abubakar na kai kara kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben 2019 da aka kammala, Mr Galadima ya ce: "kamar yadda kotun koli ta yanke hukunci kan zaben johohin Rivers da Akwa Ibom, da Jonathan ya je kotu, da akwai yiyuwar ya samu nasara, don haka zuwa kotun ba wai bakon lamari ba ne."

KARANTA WANNAN: Mutuwar dan majalisa: INEC ta yi abun azo a gani kan matakin sake zabe - APC

Zaben shugaban kasa 2015: Jonathan ne ya kashe kansa na kin zuwa kotu - Buba Galadima
Zaben shugaban kasa 2015: Jonathan ne ya kashe kansa na kin zuwa kotu - Buba Galadima
Asali: UGC

Idan ba a manta ba, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta, Alhaji Atiku Abubakar sun maka shugaban kasa Muhammadu Buhari kotu kan kalubalantar sakamakon jarabawar WAEC dinsa.

Wannan ya biyo bayan karar da jam'iyyar da Atiku suka shigar a ranar Litinin inda suka kalubalanci nasarar Buhari da APC a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru.

Atiku dai ya bukaci kotun da ta kori shugaban kasa Buhari tare da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, kasacewar a cewarsa, Buhari bai da ikon tsayawa takara saboda rashin sahihin sakamakon jarabawar WAEC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel