Abun da ya sa muka je kotu muna kalubalantar zaben Shugaba Buhari - Obi

Abun da ya sa muka je kotu muna kalubalantar zaben Shugaba Buhari - Obi

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019 da ya gabata a Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya bayyana dalilin da yasa jam'iyyar sa ta PDP da kuma dan takarar shugaban kasar suka garzaya kotu bayan zabe.

Mista Obi a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a garin Abuja dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman a kan harkokin yada labarai, abun da ya fi dacewa a demokradiyyance shine wanda duk bai yadda da sakamakon zabe ba ya tafi kotu neman hakkin sa.

Abun da ya sa muka je kotu muna kalubalantar zaben Shugaba Buhari - Obi
Abun da ya sa muka je kotu muna kalubalantar zaben Shugaba Buhari - Obi
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari yayi fatali da kudurori 2 daga majalisa

Legit.ng Hausa ta kuma samu cewa a cikin sanarwar, Mista Obi ya yabawa dan takarar shugabancin kasar, Alhaji Atiku Abubakar wanda ya kwatanta da wani bango da ginshiki da yake rike da demokradiyyar Najeriya tun shekaru 16 da suka gabata.

A wani labarin kuma, Sanatocin Najeriya a majalisar dattawan kasar a ranar Talata tayi jimamin mutuwar wasu 'yan Najeriya a hatsarin jirgin saman Itofiya da ya rutsa da su mai lamba ET 302 a satin da yagabata ciki hadda wani fitaccen Farfesa.

Farfesa Pius Adesanmi na adabi a wata jami'ar kasar Kanada kuma dan asalin kasar Najeriya da Mista Abiodun Bashuwa na cikin manyan 'yan Najeriya da hatsarin ya rutsa da su cikin jirgin mai kirar Boeing 737.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel