Mutuwar dan majalisa: INEC ta yi abun azo a gani kan matakin sake zabe - APC

Mutuwar dan majalisa: INEC ta yi abun azo a gani kan matakin sake zabe - APC

- Jam'iyyar APC a jihar Filato ta jinjinawa INEC akan matakin da ta dauka na gudanar da zaben cike gurbin kujerar zababben dan majalisar dokoki da ya mutu

- Idan za a iya tunawa Mr Ezekiel Afon, dan majalisa mai wakiltar mazabar Pengana a majalisar dokokin jihar ya mutu bayan sake zabarsa

- APC ta ce ta na zaman jiran ranar da INEC za ta sanya domin gudanar da zaben cike gurbin, bayan da hukumar zaben ta amince da korafin karin wa'adin

Jam'iyyar APC a jihar Filato ta jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC akan matain da ta dauka na sake gudanar da zaben cike gurbin kujerar wani zababben dan majalisar dokoki da ya mutu bayan zabensa.

Idan za a iya tunawa Mr Ezekiel Afon, dan majalisa mai wakiltar mazabar Pengana a majalisar dokokin jihar ya mutu bayan sake zabarsa.

INEC ta sanya ranar 23 ga watan Maris, ranar da za a sake gudanar da zaben gwamnan jihar zagaye na biyu, ta zamo ranar cike gurbin kujeran dan majalisar, sai dai hukumar ta canja ranar bayan da APC ta roki karin lokaci.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: PDP ta yi taro kan samun shugabancin majalisar tarayya

Mutuwar dan majalisa: INEC ta yi abun azo a gani kan matakin sake zabe - APC
Mutuwar dan majalisa: INEC ta yi abun azo a gani kan matakin sake zabe - APC
Asali: UGC

Chief Letep Dabang, shugaban jam'iyyar APC na jihar Filato ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Laraba a garin Jos cewa jam'iyyar ta nuna rashin amincewarta da ranar Asabar da hukumar ta sanya domin gudanar da zaben cike gurbin kujerar dan majalisar.

"Mun yi mamakin yadda aka sanya ranar zaben cike gurbin da ranar zaben gwamnan jihar zagaye na biyu. A wajenmu, zaben cike gurbi da zaben gwamnan zagaye na biyu suna da banbanci sosai.

"Idan har ana batun zaben cike gurbi, to ana baiwa jam'iyyu kwanaki 90 domin su shirya, da kuma gudanar da zaben fitar da gwani," a cewar sa.

Dabang ya ce suna zaman jiran ranar da INEC za ta sanya domin gudanar da zaben cike gurbin, bayan da hukumar zaben ta amince da korafin da suka gabatar mata na karin wa'adi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel