Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje

Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje

A daidai lokacin da ake saura yan kwanaki kadan kafin karashe zaben gwamnan jihar Kano, jama’ar mazabar Gama wacce kuri’unta ne zai yanke hukuncin zaben, sun tashi sun ga gwamnati na aiwatar da manyan ayyuka na ci gaba a yankinsu.

An tattaro cewa mutanen yankin sun ce sun shafe shekaru da dama suna fama da kalubale na karancin ruwa, hanyoyi, asibitoci da dai suransu ba tare da sun samu agaji daga gwamnati ba.

Sai dai a yanzu haka gwamnati ta fara aikin gina fanfon burtsatse guda 11 a wannan yanki na gama domin shawo kan wannan matsala ta karancin ruwa.

Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje
Dalilin da ya sa nake aiki a Gama kafin zabe – Ganduje
Asali: Twitter

Hakazalika ana kan yin aikin hanya da aka fara a baya, ba tare da an kamala ba, duk a gabanin zaben cike gibi na 23 ga watan Maris.

Sai dai wasu al'umma a ciki da wajen gundumar na ganin cewa gwamnatin ta fara wadannan ayyuka ne domin neman kuri'a a zaben na ranar Asabar.

Tuni dai aka samu rahotanni na sayen kuri'a a yankin, inda rundunar 'yan sanda a jihar ta bayar da sanarwar kame wasu da ake zargi da sayen katunan zabe a wurin al'umma.

KU KARANTA KUMA: Ban taba tsoma baki na cikin harkar zaben Gwamna Jihar Kano ba – Tinubu

Sai dai Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a hira da yayi da shafin BBC ya ce ayyukan da ake yi suna cikin wadanda gwamnati ta tsara tun fil-azal.

A cewar sa "wannan aiki dama yana kan layi, amma a wannan karo ne Allah Ya sa za a yi shi yanzu."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel