Babbar magana: PDP ta yi taro kan samun shugabancin majalisar tarayya

Babbar magana: PDP ta yi taro kan samun shugabancin majalisar tarayya

- Zababbun sanatocin PDP sun gudanar da wani taro a Abuja domin tattaunawa kan rikicin shugabanci a Majalisar Tarayyar Kasar ta 9

- Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa taron na daga cikin shirye shiryen jam'iyyar na samun shugabancin majalisar tarayyar

- Jam'yyar PDP na da zababbun sanatoci 43 a majalisar tarayyar ta 9, yayin da jam'iyyar APC ke da zababbun sanatoci 65

Rahotannin da Legit.ng ta samu na nuni da cewa, zababbun sanatocin Jam’iyyar PDP sun gudanar da wani taro a babban birnin tarayya Abuja, a daren ranar Talata domin tattaunawa kan rikicin shugabanci a Majalisar Tarayyar Kasar ta 9.

Majiya ta shaidawa Daily Trust cewa taron na daga cikin shirye shiryen jam'iyyar na samun shugabancin majalisar tarayyar.

Rahotanni sun bayyana cewa zababbun sanatocin PDP na son yin yarjejeniya tare da tsayar da mutum daya da zai iya karawa da dan takarar da APC za ta tsaida, da tunanin cewa abunda ya faru a 2015 zai sake faruwa inda daya daga cikinsu, Ike Ekweremadu ya zamo mataimakin shugaban majaisar dattijan duk da cewa APC ce mai mafi rinjaye.

KARANTA WANNAN: Udoma ya bayyana yadda gwamnatin Nigeria ta tsara biyan mafi karancin albashi

Babbar magana: PDP ta yi taro kan samun shugabancin majalisar tarayya
Babbar magana: PDP ta yi taro kan samun shugabancin majalisar tarayya
Asali: UGC

Akwai jita jitar cewa zababbun sanatocin PDP za su iya zabar daya daga cikin sanatoci ukku da ke harin kujerar majalisar dattijan daga shiyyaar Arewa maso Gabas, da suka hada da Ahmad Lawan, Ali Ndume da kuma Danjuma Goje.

Wata majiya wacce ke da masaniya kan abubuwan da ke faruwa ta bayyana cewa zababbun sanatocin PDP za su iya fin raja'a akan Goje kasancewar yana da kusanci sosai da Saraki kuma yana daya daga cikinsu.

Jam'yyar PDP na da zababbun sanatoci 43 a majalisar tarayyar ta 9, yayin da jam'iyyar APC ke da zababbun sanatoci 65.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel