Buhari ya tafi Umara, ya mika Najeriya hannun Osinbajo - Rahotanni

Buhari ya tafi Umara, ya mika Najeriya hannun Osinbajo - Rahotanni

Wasu rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya, kasa mai tsarki don gudanar da Ibadan aikin Umrah, kuma tuni ya mika ragamar kula da Najeriya a hannun mataimakinsa Yemi Osinbajo.

Wadannan rahotanni sun karade shafukan sadarwar zamani, musamman na Facebook da na Twitter, sai dai yayin da wasu rahotanni suke nuni da cewa a yammacin Talata ne Buharin ya wuce, wasu rahotannin kuma cewa suka yi a yau Laraba ne zai wuce.

KU KARANTA: Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Mai martaba Sarkin Patigi ya rasu

Buhari ya tafi Umara, ya mika Najeriya hannun Osinbajo - Rahotanni
Buhari a Umrah a 2016
Asali: UGC

Sai dai manya manyan hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari basu tabbatar da hakan ba, kuma basu bayyana hakan a shafukansu na sadarwar zamani ba, daga cikin hadiman da Legit.ng ta bibiya akwai Garba Shehu da Femi Adesina.

Sauran hadiman da muka bibiya sun hada da Buhari Sallau da Bashir Ahmad, da kuma shi kansa shafin kafar sadarwar zamani na Facebook na shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma babu makamanciyar wannan magana, sai dai babu wanda ya karyata rahotannin kuma.

Aikin Umrah da shugaba Buhari ya je na karshe shine a watan Feburairu na shekarar 2016, inda ya samu rakiyar gwamnonin jihohin Ogun, Zamfara, Katsina da Osun, da kuma mashawarcinsa akan harkar tsaro Babagana Munguno.

Sai dai yan Najeriya sun bayyana ra’ayinsu mabanbanta game da wannan rahoton zuwa Umrah na Buhari, yayin da wasu ke ganin hakan yayi daidai, wasu kuma cewa suke yi akan me zai fita daga Najeriya yayin da ake samun kashe kashe a Zamfara, ga kuma zaben maimaici na zaben gwamna a jihohi 6 na karatowa?

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel