Ban taba tsoma baki na cikin harkar zaben Gwamna Jihar Kano ba – Tinubu

Ban taba tsoma baki na cikin harkar zaben Gwamna Jihar Kano ba – Tinubu

Babban Jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, yayi magana game da zaben gwamna da za a karasa a jihar Kano. Bola Tinubu yayi wannan jawabi ne Ranar Talata 19 ga Watan Maris.

Asiwaju Bola Tinubu yace sam ba ya tsoma bakin sa a cikin harkar zaben Kano. Jagoran na APC ya karyata cewa yana jihar Kano domin ganin gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje ya san yadda yayi ya koma kan kujerar sa.

Bola Tinubu ya fadawa jaridar Premium Times cewa rade-radin da ake yi na cewa ya tafi jihar Kano, ba gaskiya bane. Tinubu yayi wannan jawabi ne ta bakin babban Hadimin sa da ke magana da yawun sa watau Tunde Rahman.

A jawabin da Hadimin na Tinubu ya fitar, ya bada tabbacin cewa ko sau daya Mai gidan na sa bai zo Kano ba. Tsohon gwamnan yake cewa hoton sa da Abdullahi Ganduje da ake ta yadawa, tsohon hoto ne da aka dauka tun kwanaki.

KU KARANTA: Wani Shehin Malami yayi magana a kan zaben Gwamnan Jihar Kano

Ban taba tsoma baki na cikin harkar zaben Gwamna Jihar Kano ba – Tinubu
Babban Jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Tinubu da Gwamnan Kano
Asali: Facebook

Cif Bola Tinubu yake cewa an dauki wannan hoto da ake ta ya-ma-di-di da shi ne a Legas lokacin da gwamnan jihar da mukarraban sa su ka kai wata ziyara zuwa kasar Yarbawa. Tinubu yace babu abin da zai sa ya shiga cikin harkar siyasar Kano.

Babban Jagoran na APC yake cewa wasu Makiyan sa ne kurum su ke shirya masa irin wadannan karya kamar yadda su ka rika yada labari cewa PDP za ta karbe Legas a lokacin da aka yi zaben shugaban kasa da kuma gwamnan jihar na bana.

Tinubu ya nuna cewa wasu manyan PDP ne su ka rika cusa kan su cikin zaben Legas da bai shafe su ba, amma duk da haka yace bai fito yayi magana ba. Tinubu yace shi mutum ne da yadda da damukaradiyya kuma ya yarda da zabe na adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel