INEC za ta yanke hukuncin karshe akan Rivers da Bauchi a yau

INEC za ta yanke hukuncin karshe akan Rivers da Bauchi a yau

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jiya Talata, 19 ga watan Maris ta ce za ta dauki hukuncin karshe akan ci gaba da tsarin zabe a jihar Rivers a yau.

Har ila yau ya dangana da irin hukuncin da kotu da za ta yanke a yau, INEC za ta samu matsaya bayan ta yi biyayya ga umurnin kotun da dakatar da tattara sakamako a jihar Bauchi.

A bangaren Rivers, an tattaro cewa INEC za ta saki hukuncin karshe kan ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna, wanda ya tsayar a baya biyo bayan tsaiko da ta samu.

INEC za ta yanke hukuncin karshe akan Rivers da Bauchi a yau
INEC za ta yanke hukuncin karshe akan Rivers da Bauchi a yau
Asali: Facebook

Babban sakataren labaran Shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, yace hukumar za ta saki ka’idoji don ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Rivers da kuma kamala sakamakon zaben gwamna daga karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, ta bayyana cewa tana kalabulantar hukuncin da kotu ta yanke jiya Talata 20 ga Watan Maris, na hana ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamna da aka yi a Bauchi.

INEC ta garzaya kotu ne bayan da wani babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya bada umarnin cewa a dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi da aka yi a Yankin Tafawa-Balewa makonni 2 da su ka wuce.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai game da harkar zabe na INEC, Festus Okoye, ya bayyanawa manema labarai cewa sun daukaka kara inda su ke neman a kyale hukumar ta cigaba da kiddiga kuri’un zaben Bauchi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel