PDP tayi karar Justice Inyang Ekwo saboda dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi

PDP tayi karar Justice Inyang Ekwo saboda dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi karar Justice Ekwo Inyang na babban kotun tarayya bisa dakatar da kirga kuri'un zaben gwamna na Bauchi inda ta ce kotun sauraron kararrakin zabe na kawai ta ke da ikon aikata hakan kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Jam'iyyar ta ce hukuncin da alkalin ya yi na dakatar da Hukumar Zabe INEC daga karrasa zaben gwamna na jihar Bauchi, Justice Inyang ya sabawa sashi na 87(11) na dokar Zabe wadda ta ce babu kotun da ke da ikon dakatar da zabe muddin an shigar da kara a wata kotun.

A takardan korafin shugaban PDP Prince Uche Secondus ya rattaba hannu a kai a Abuja, jam'iyyar ta ce tattara kuri'u da bayyana wanda ya lashe zabe abu ne da ke faruwa bayan an kammala zabe saboda haka hurumi ne na kotun sauraron kararrakin zabe.

PDP tayi karar alkalin da ya dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi
PDP tayi karar alkalin da ya dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta saka sharadin biyan sabon albashi na N30,000

Ga wani sashi daga cikin karar, "Duk da tanadin da doka tayi, Justice Ekwo ya saurari karar Alhaji Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC cikin sa'o'i 24 a ranar 19 ga watan Maris kuma ya bawa INEC umurnin dakatar da zaben Bauchi har sai ya yanke hukunci.

"Kirga kuri'u bayan zabe ake yin shi kuma a karkashin sashi na 87(11) na Dokar Zabe, babu wata kotu da ke da ikon tsayar da wani zabe a yayin da akwai wata karar a kotu.

"Alkalin Alkalan na Najeriya ya kafa kotunan sauraron kararrakin zabe a jihohi daban-daban da za suyi shari'a a kan matsalolin da za su taso bayan zabe saboda hakan hukuncin Justice Iyang Ekwo ya sabawa doka kuma ya tauye hakkin al'ummar karamar hukumar Tafawa Balewa da jihar Bauchi."

Jam'iyyar na PDP ta bukaci Cibiyar Shari'a na kasa ta ceto demokradiyar mu ta hanyar daukan matakin gaggawa a kan saba dokar da Justice Inyang ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel