Gwamnan Jihar Katsina ya gana da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Gwamnan Jihar Katsina ya gana da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya gana da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Ranar Talata 20 ga Watan Maris a ofishin sa da ke cikin fadar shugaban kasa a birnin Tarayya Abuja.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya tattauna da mataimakin shugaban kasar ne inda ya kuma taya sa murnar nasarar da ya samu na sake lashe zaben da aka yi bana. Gwamna Aminu Masari yace sun yi magana game da matsalar tsaro.

Gwamnan na Katsina yace ya kai kukan sa a game da daukar jama’a da ake yi ana garkuwa da su, da kuma satar dabobbi da ya addabi jama’an sa. Gwamnan yace zai kuma gana da Sufeta Janar na ‘Yan Sanda da shugaban hukumar DSS.

KU KARANTA: Yadda aka sace wasu Jagorin APC ana shirin zabe a Jihar Ribas

Gwamnan Jihar Katsina ya gana da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo
Gwamnan Katsina tare da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo
Asali: Facebook

Aminu Masari ya kuma bayyana cewa da shi aka gana da hafsun sojojin kasar a dalilin irin yadda aka maida satar mutane ruwan dare a jihar ta Katsina. Gwamnan na APC ya bayyanawa manema labaran da ke cikin Aso Villa wannan.

Masari ya nuna cewa jibge jami’an tsaro kurum ba zai kawo karshen rashin tsaro a jihar ba, don haka yace akwai bukatar ayi amfani da dabaru na musamman. Gwamnan yace zai gana da manyan hafsoshin tsaro kafin ya koma jihar sa.

A karshe gwamnan na jihar shugaban kasa, yayi magana game da sake zaben sa da mutanen Katsina su kayi, Aminu Masari yace yayi wa jama’an sa aiki ne don haka su ka nemi ya zarce a zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel