Ana kishin-kishin cewa kwanan nan za a nada sabbin shugabannin tsaro

Ana kishin-kishin cewa kwanan nan za a nada sabbin shugabannin tsaro

Yayinda wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko ke zuwa karshe, akwai alamun cewa nan ba da jimawa ba za a nada sabbin shugabannin tsaro.

Buhari zai dau rantsuwar aiki a ranar 29 ga watan Mayu a karo na biyu, bayan lashe zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 da watan Fabrairu da aka yi.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa yawan ganawa daban-daban da shugaba Buhari ke ta yi da shugabannin tsaro na daga cikin tsarin ritaya da za a yi masu domin su bar kujerarsu, wanda ake sanya ran zai kasance a karshen wannan mulki ko kuma bayan rantsar da Shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

Ana kishin-kishin cewa kwanan nan za a nada sabbin shugabannin tsaro
Ana kishin-kishin cewa kwanan nan za a nada sabbin shugabannin tsaro
Asali: Twitter

Shugabannin tsaro da abun zai shafa sun hada da Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai; Shugaban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Etete-Ibas da kuma Shugaban hafsan sojin sama, AVM Sadique Abubakar. An nada su ne a shekarar 2015.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai

Wata majiya daga hedkwatar tsaro ta fada ma jaridar Daily Sun cewa shugabannin tsaron, wadanda aka sha tsawaita wa’adinsu na sane da cewa za a iya maye gurbinsu da wasu a kowani lokaci sannan sun shirya mika shugabanci.

An tattaro cewa tuni an rubuta sunayen jami’an da za a iya kwasa a matsayin sabbin shugabannin tsaro sannan an tattance su ba tare da saninsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel