'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai

'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai

- Yankin Arewa ta tsakiya na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakilai

- Mambobin majalisa daga yankin sun ce basu wannan matsayi zai tabbatar da cewar ana yi da su a majalisar da kuma ingancin kalmar daidaito a majalisar

- Wani mamba daga yankin yace sun taka muhimmiyar rawar gani ga jam'iyyar APC a lokacin zaben kasar don haka sun cancanci tukwacin wannan kujera

Masu ruwa da tsaki a majalisar wakilai daga arewa maso tsakiya sun bukaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta kai matsayin kakakin majalisa yankin arewa ta tsakiya domin nuna daidaito.

“Duba ga wakilci daga yankinmu, mun cancanci matsayin kakakin majalisa kamar yadda yan yankin arewa maso yamma da kudu maso yamma suka samu matsayin Shugaban kasa da na mataimakin Shugaban kasa."

'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai
'Yan Arewa su na neman a ba su kujerar Shugaban Majalisar Wakilai
Asali: Twitter

Dyegh yayi bayanin cewa “ba yankin arewa maso tsakiya matsayin kakakin majalisa zai tabbatar da ingancin daidaito.

“Mun kula cewa baya ga arewa maso yamma da arewa maso gabas, arewa ta tsakiya ta taka wa jam’iyyar rawar gani sosai a zaben kasar da aka yi don haka akwai bukatar saka masu akan wannan kokari da biyayya da suka yi.

“Yankin arewa ta tsakiya za taga cewa ana tafiya tare da ita idan har aka bari ta samar da kakakin majalisar wakilai na gaba."

KU KARANTA KUMA: Kujerar mataimakin shugaban majalisa: Uwargidar Tinubu ta samu matsala, mijinta bai goyon bayanta

Sai dai a lokacin zauren tambaya da amsa, dan majalisa Solomon Maren na PDP ya fada ma manema labarai cewa an tattauna da shi saboda “lamari ne na yanki don haka ina daga ciki”.

Maren ya kara da tabbatar da cewa duk da cewar kakakin majalisa mai barin gado, Yakubu Dogara dan PDP ne yana iya shiga tseren a matsayin mamba na marasa rinjaye a majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel