Kujerar mataimakin shugaban majalisa: Uwargidar Tinubu ta samu matsala, mijinta bai goyon bayanta

Kujerar mataimakin shugaban majalisa: Uwargidar Tinubu ta samu matsala, mijinta bai goyon bayanta

Manufar Sanata Oluremi Tinubu, yar majalisar dattawa mai wakiltan Legas ta tsakiya, na takarar kujerar mataimakiyar shugaban majalisar dattawa ya samu cikas yayinda maigidanta, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna baya goyon bayanta.

Game da binciken da Daily Independent ta gudanar, Tinubu ya fi bukatan samun kakakin majalisar dattawa daga Legas, wanda yake son a baiwa dan majalisa, Femi Gbajabiamila, fiye da kujerar mataimakin shugaban majalisan dattawa.

Majiya mai karfi ya bayyawa cewa ba zai yiwu a zabi mataimakin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai duk daga jihar Legas ba.

Kokarin Tinubu wajen tabbatar da cewa Femi Gbajabiamila ya zama kakakin majalisar wakilai ya samu cikas ne a shekarar 2015 inda kakakin majalisar na yanzu, Yakubu Dogara, ya hada baki da yan jam'iyyar PDP.

Wani majiya daga cikin majalisar wakilai wanda sabon dan majalisa ne ya ce Tinubu na iyakan kokarinsa wajen ganin cewa abinda ya faru a Yunin 2015 bai maimaita kansa ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun addabemu, abin ya ishemu - Mazauna Askari-Uba

Yace: "Hakane, bukatar Sanata Oluremi Tinubu, na neman kujerar mataimakiyar shugabar majalisa gaskiya ne, kasancewarta kwararriyar yar majalisa, amma hakan ya ci karo da bukatar maigidanta wanda ke kokarin ganin cewa Legas ta kawo kakakin majalisar wakilai."

"Akwai yiwuwan APC ta baiwa yankin kudu maso yamma kujerar majalisa kamar yadda tayi a 2015, kuma dan takararmu shine Femi Gbajabiamila, shugaban masu rinjaye na yanzu."

"Tinubu bai wani damu da uwargidarsa ta zama mataimakiyar shugabar majalisar dattawa ba, saboda hakan ka iya zama cikas ga kujerar kakakin da ake son Gbajabiamila ya samu."

Wani jigon jam'iyyar ya kara da cewa Tinubu bai tattauna al'amarin uwargidarsa ba, amma da kamar wuya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel