Kashe kashe a Zamfara: Buhari da Yari sun goga gemu da gemu a Villa

Kashe kashe a Zamfara: Buhari da Yari sun goga gemu da gemu a Villa

Gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ya kai ziyara fadar shugaban kasa inda ya samu damar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka tattauna akan matsalar tsaro data addabi jahar Zamfara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yari ya kai wannan ziyara ne a ranar Talata, 19 ga watan Maris, inda bayan ganawar tasa da Buhari ya shaida ma manema labaru cewa ya kawo ma Buhari korafi ne akan yadda yan bindiga ke cigaba da tara makamai.

KU KARANTA: Ka fito mu buga idan ba ga tsoro ba – Sojoji sun kalubalanci Shekau

Kashe kashe a Zamfara: Buhari da Yari sun goga gemu da gemu a Villa
Gwamna Yari
Asali: UGC

A jawabinsa, Gwamna Yari ya bayyana cewa babu sauran maganan sulhu tsakanin gwamnati da yan bindiga a jahar Zamfara. “Na fada ma jama’a cewa babu sauran sulhu, saboda sau uku ina neman sulhu dasu, amma bai haihar da 'da mai ido ba.

“A zamanmu na farko mun gayyaci Sojoji, DSS, Yansanda, babban mai tsaron gwamna, da wasu Sarakunan gargajiya, kuma mun ga irin makaman da suke amfani dasu, hatta jami’an tsaron dake Zamfara basu da kamarsu.

“A wuri daya kacal mun samu bindigar AK 47 fiye da guda 500, yayin da a Zamfara bamu da AK 47 guda 90, don haka da muka yi musu tayin sulhu, sai suka ki amincewa.” Inji gwamnan.

Haka zalika gwamnan ya kara da cewa idan rani yazo, sais u fara neman ayi sulhu saboda sun san Sojoji na iya cimmasu a duk inda suka boye a cikin daji, amma da zarar an ce damuna ta sauka, shikenan sai su koma cikin daji.

Daga karshe Gwamna Yari ya bada tabbacin gwamnatin tarayya zata mike tsaye akan wannan matsala ta hanyar tura karin dakarun Sojoji tare da basu sabbin makamai na zamani domin fatattakar yan bindigan daga jahar tare da kawo karshen ayyukansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel