Boko Haram sun addabemu, abin ya ishemu - Mazauna Askari-Uba

Boko Haram sun addabemu, abin ya ishemu - Mazauna Askari-Uba

Wasu mazauna kauyen Multafu a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno sun kawo kuka kan hare-haren da Boko Haram ke kawo musu tsawon mako daya yanzu. Sun bayyana jimaminsu kan garkuwa da yaynsu mata biyu da yan Boko Haram sukayi.

Wannan na kunshe cikin jawabin da wani dattijon garin ya saki, Mr Fali Ijudigal, a ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2019.

Garin Multafu wata kauye ce da aka sani da yan kabilar Marghi kuma yawancinsu manoma ne. Kana sun hada iyaka da dajin Sambisa.

A ranar 10 ga watan Maris misalin karfe 10, yan ta'addan sun kai hari Multafu inda suka hallaka jami'in kato da gora yayinda mazauna da dama suka jikkata.

Kana sun babbaka gidajensu da wuta, sun kwashe musu kayan abinci, daruruwan sun gudu daga muhallansu kuma anyi garkuwa da yan mata biyu, Stella Ibrahim da Godiya Ibrahim.

KU KARANTA: Mun bankado sabon shirin da APC keyi na tunbuke Sarkin Musulmi da Sarkin Kano - CUPP

Yace: "Mu mazauna Multafu na nuna damuwarmu kan yawan hare-haren da yan ta'adda ke kawo mana. Garin Multafu ta fuskanci hari daga Boko Haram ranar Lahadi, 10 ga watan Maris 2019 misalin karfe 10 na dare. Wani jami'in kato da gora dake kokarin taimakonmu ya rasa rayuwarsa yayinda motar hukumar CJTF ta taka wata Bam da yan Boko Haram suka dasa."

"An sace yan gida daya, Stella Ibrahim mai shekaru 21 da Godiya Ibrahim mai shekaru 16 a ranar, kuma har ila yau babu labarinsu. An kona gidaje, mutane da dama sun jikkata kuma jama'a sun gudu."

"Wani abin takaicin shine babu yunkuri daga gwamnati, jami'an tsaro ko wata hukumar da ke da hakkin kawo agaji. Kana babu wanda ya zo mana jaje. Duk da cewa jama'ar Multafu sun fito kwansu da kwarkwatansu wajen zaben APC a zaben shugaban kasa, yan majalisar dokokin kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel