Ka fito mu buga idan ba ga tsoro ba – Sojoji sun kalubalanci Shekau

Ka fito mu buga idan ba ga tsoro ba – Sojoji sun kalubalanci Shekau

Dakarun Sojin Najeriya sun yi kira ga shugaban bangaren kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da sauran mayakansa dasu fito ayi gaba da gaba don yin fadan karshe idan ba ga tsoro ba, kamar yadda suka bayyana a cikin wani bidiyo.

Legit.ng ta ruwaito wani jami’in Sojan Najeriya ne ya daura bidiyon a shafinsa na Instagram mai suna @officialbennision, wanda dama ya saba daura bidiyoyin ayyukan Sojoji a shafinnasa don mabiyansa su kalla.

KU KARANTA: Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama

A cikin wannan bidiyo dai an jiyo wani Soja yana kira ga mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram dasu fito a buga, yana cewa “Boko Haram ku fito mu buga, idan baku fito ba ba zamu tashi daga nan ba, don haka dole ku fito muyi fadan karshe. Allahu Akbar.”

Ya cigaba da cewa “Na dauka kuna da karfi, don haka ai sai ku fito mu buga, idan bamu yi fada ba ba zamu tashi daga nan ba, kun ji ko? Idan baku fito ba, ba zamu tashi daga nan ba, Allahu Akbar”

A wani labarin kuma Boko Haram ta kaddamar da wata mummunan hari a kokarinsu na afkawa cikin garin Michika na jahar Adamawa tare da kokarin karbe garin, sai dai sun samu tirjiya daga dakarun rundunar Sojin kasa.

Mazauna garin Michika sun bayyana cewa da misalin karfe 7 na daren jiya suka fara jin karar harbe harbe daga kan hanyar Michika zuwa Lasa, daidai lokacin da Sojoji suke shan artabu da yan Boko Haram kenan.

Shima wani mazaunin kauyen Bazza dake kusa da garin Michika, John Jigalambu ya tabbatar da aukuwar harin, inda yace daga kauyensu suna jiyo karar musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram da Sojoji, hakan tasa kafatanin jama’an kauyen tserewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel