Wani babban dan siyasa ne ya biyamu don mu halaka Ahmad Sulaiman – Masu garkuwa

Wani babban dan siyasa ne ya biyamu don mu halaka Ahmad Sulaiman – Masu garkuwa

Shugaban miyagun barayin da suka yi garkuwa da fitaccen mahaddacin Al-Qur’anin nan, Alaramma Ahmad Sulaiman ya bayyana cewa wani babban dan siyasa daga jahar Kebbi ne ya biyasu donsu halaka shi, inda yace naira miliyan dari uku ya biyasu.

Legit.ng ta ruwaito shugaban barayin ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da wani aminin Malamain ta wayar tarho, inda ya nemi sai an biyasu akalla naira miliyan 300, da kuma kudin man da suka kona kafin su saki Alaramma.

KU KARANTA: Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama

Wani babban dan siyasa ne ya biyamu don mu halaka Ahmad Sulaiman – Masu garkuwa
Ahmad Sulaiman
Asali: UGC

“Babu matsala idan babu kudi, mu ba saboda kudinsa muka rike shi ba, mu kudi aka bamu mu kashe shi, don wanda ya bamu aikin ya ce shi dan ta'adda ne. Abunda ya sa har muka yi labarin kudi, bayan mun kama shi, mun fahimci rahoton da aka bamu akansa ba haka bane.

"Wannan abu daga sama ne, harkar siyasa ce, ba zan boye ko munafunci ba, daga Birnin Kebbi muka biyo shi. Abunda aka ce mana dan ta'adda ne mu kashe shi, ko da muka kama shi, muka duba gemun shi, muka ga wannan bai yi kama da dan ta'adda ba.” Inji shi.

Sai dai shugaban barayin ya tabbatar ma wanda suke wayar da cewa wanda ya daukesu sojan hayan kashe Alaramma ya riga ya biyasu, kuma yayi alkawarin ninka musu wadannan kudade, don haka babu yadda za’ayi su ci masa kudi ba tare da sun cika masa aiki ba.

"Abu daya da zamu yi, ba mu ci mishi kudi ba mu yi mishi aiki ba, don haka ya maida masa kudinsa sannan ya bamu na mai, ba wani abu sai mu barshi. Wancan bai yiyuwa mu ci mishi dukiyarshi bamu yi mishi aiki ba, kuma ya ji mun kama shi ba wai ba mu kama shi ba.

“Yan Siyasarku akwai 'yan matsaloli, akwai munafukai daga ciki. Abunda ya bamu miliyan dari uku (300) don mu kashe shi, ya ce dan ta'adda ne, sannan idan muka kashe shi fiye da wannan ma zai kara mana.” Inji shi.

Daga karshe shugaban ya tabbatar ma aminin Alaramma cewa basu taba lafiyarsa ba har yanzu, amma fa ba suce lallai sai an kawo kudin ba, domin dama kasheshi aka ce suyi, don haka sai dauki matakin daya kamata akansa idan har ba’a biyasu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel