Mun bankado sabon shirin da APC keyi na tunbuke Sarkin Musulmi da Sarkin Kano - CUPP

Mun bankado sabon shirin da APC keyi na tunbuke Sarkin Musulmi da Sarkin Kano - CUPP

Gamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya CUPP a ranar Talata ta bayyana cewa sun bankado sabon shirin da APC keyi na tunbuke Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Sun kara da cewa jigogin jam'iyyar All Progressives Congress APC a Sokoto da Kano ke shirya wannan kaidi.

Kakakin gamayyar, Imo Ugichinyere, ya yi wannan tuhuma a jawabin da ya baiwa manema labarai a Abuja.

Ugochinyere ya yi ikirarin cewa an shirya tsige sarakunan ne saboda bangarancin da suka nuna kan zabe zagaye na biyu da za'a gudanar a jihohin Sokoto da Kano ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA: Atiku kuri'u 18,356,732 ya samu yayinda Buhari ya samu 16,741,430 - Lauyoyin PDP

Yace: "Gamayyar jam'iyyun adawa ta sake bankado labarin leken asiri kan wani tuggu da jigogin APC a Kano da Sokoto ke shiryawa tare da goyon bayan Adams Oshiomole kan Sarkin Musulmi da Sarkin Kano."

"Muna sanar da yan Najeriya cewa wannan shiri da barazana da shugabannin jam'iyyar APC keyi na cire mai alfarma sarkin Musulmi da Sarkin Kano saboda sun ki nuna bangaranci a karashen zaben da za'a gudanar a Kano da Sokoto."

"Shugabannin APC na tuhumar sarakunan da zargin cewa suna goyon bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP kuma sun shirya cewa muddin sarakunan gargajiyan basu goya musu baya wajen murde zabe ba, za'a kwance musu rawani."

A baya, jam'iyyar PDP ta yiwa APC zargin yunkurin cire sarkin Musulmi amma ta musanta hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel