Hukumar INEC ta sheka Kotu bayan an hana ta tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa

Hukumar INEC ta sheka Kotu bayan an hana ta tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa

Hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, ta bayyana cewa tana kalabulantar hukuncin da kotu ta yanke jiya Talata 20 ga Watan Maris, na hana ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamna da aka yi a Bauchi.

INEC ta garzaya kotu ne bayan da wani babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya bada umarnin cewa a dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi da aka yi a Yankin Tafawa-Balewa makonni 2 da su ka wuce.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai game da harkar zabe na INEC, Festus Okoye, ya bayyanawa manema labarai cewa sun daukaka kara inda su ke neman a kyale hukumar ta cigaba da kiddiga kuri’un zaben Bauchi.

KU KARANTA: Shehin Malami yayi kira ga babbar murya a kan zaben Gwamnan Kano

Hukumar INEC ta sheka Kotu bayan an hana ta tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa
Kotu ta hana INEC sanar da wanda ya ci Gwamnan Bauchi jiya
Asali: Instagram

Okoye yace su na kalubalantar wannan mataki da kotu ta dauka ba tare da hurumin ta ba. INEC tace duk da an dakatar da tattara kuri’un zaben gwamna, za a cigaba da aiki a kan zaben majalisar dokokin na yankin na Tafawa Balewa.

Yanzu dai hukumar tace ta yi wa umarnin kotu biyayya amma za ta maka na ta karar na dabam a gaban kuliya domin a rushe hukuncin da Alkali Inyang Ekwo ya dauka bayan gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar ya shigar da kara.

Hukumar INEC ta dauki matakin fasa gudanar da zaben cika-gibi a jihar Bauchi ne bayan wani zama da tayi, inda tace za ta tattara sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa ta fadi wanda ya ci. Wannan ya sa APC ta kai kara kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel