Atiku kuri'u 18,356,732 ya samu yayinda Buhari ya samu 16,741,430 - Lauyoyin PDP

Atiku kuri'u 18,356,732 ya samu yayinda Buhari ya samu 16,741,430 - Lauyoyin PDP

Wasu bayanai daga karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da Atiku Abubakar suka shigar kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasan 23 ga watan Febrairu, sun fara bayyana a ranar Talata. 19 ga watan Maris.

Lauyoyin PDP, wadanda suka bayyana cewa akwai hujjoji 50 cikin karar da suka shigar kotun zabe dake birnin tarayya Abuja inda take tuhumar hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC, shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

A ranar 27 ga wtaan Febrairu, hukumar INEC ta alanta Buhari a matsayin wanda yayi nasara a zaben da kuri'u 15,191,847 yayinda mai biye masa, Atiku, ya samu kuri'u 11,262,978.

Amma daga cikin takardun karar da aka shigar kotu PDP tace daga cikin na'urar yanar gizon INEC, sakamakon gaskiya bayan an tattaro na dukkan jihohi ya nuna cewa Atiku ya samu jimillar kuri'u 18,356,732 yayinda Buhari ya samu 16,741,430.

KU KARANTA: Yaki da hijabi: Kotu ta yankewa wata mata hukuncin bulala 148 da daurin shekaru 38

Sun kara da cewa wannan shine sakamakon zaben jihohi 35 da birnin tarayya Abuja saboda ba'a samu sakamakon zabe daga jihar Rivers ba har zuwa ranar 25 ga watan Febrairu, 2019. Saboda haka, Atiku ya lallasa Buhari da kuri'u 1,615,302.

Mun kawo rahoton cewa babban lauyan dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP. Livy Uzokwu, ya bayyana cewa lauyoyin jam'iyyar na da isassun hujjojin da zasu gabatar a gaban kotu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Yayinda yake magana da manema labarai a Abuja, Lauyan ya ce duk da cewa sun samu matsala wajen duba kayayyakin da aka gudanar da zabe da su, ba zasuyi kasa a guiwa wajen shigar da kara ba.

Atiku ya bukaci kotun ta alantasa a matsayin wanda yayi nasara a zaben 23 Febrairu ko kuma a sake sabon laale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel