Ba za mu yarda da tayar da zaune tsaye ba a Kano – Gwamna Ganduje

Ba za mu yarda da tayar da zaune tsaye ba a Kano – Gwamna Ganduje

Gabannin sake gudanar da zabe a jihar Kano a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, Gwamna Abdullahi Gandujena jihar ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da kowani yunkuri da tayar da zaune tsaye ba daga kowace kungiya ko mutum ba a jihar.

Ganduje ya yi gargadin ne a ranar Talata, 19 ga watan Maris a Kano lokacin da kungiyoyin hadin gwiwa 320 mai suna jakadun zaman lafiyar Kano suka kai masa ziyarar ban girma.

“Ba za mu yarda da tayar da zaune tsaye ba a kowani hali, sannan gwamnati ba za ta nade hannu tana kallon wasu mutane suna hargitsa jihar ba.

Ba za mu yarda da tayar da zaune tsaye ba a Kano – Gwamna Ganduje
Ba za mu yarda da tayar da zaune tsaye ba a Kano – Gwamna Ganduje
Asali: Depositphotos

“A matsayina na gwamnan jihar Kano kuma babban Shugaban tsaro a jihar, ba zan iya bacci ba idan wani jini ya zuba a banza ba.

“Ba wai ina Magana bane a matsayin dan takarar gwamna ba, a’a ina Magana ne a matsayin gwamna kuma babban Shugaban tsaro a jihar. Duk wanda ke burin tayar da rikici toh ba zai ci lafiya ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers

Kungiyar jakadun zaman lafiyar na Kano sun ba Ganduje tabbacin wanzar da zaman lafiya kafin, lokaci da kuma bayan sake zaben.

Abubakar Muhammad wanda ya jagoranci kungiyar ya yaba ma Ganduje akan furucinsa na cewa za a tabbatar da zaman lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel