Sau daya na taba ganin Dogara, shima din daga nesa: Jami'in INEC ya mayarwa APC da martini

Sau daya na taba ganin Dogara, shima din daga nesa: Jami'in INEC ya mayarwa APC da martini

Festus okoye, kwamishina na Kasa ta Hukumar zabe (INEC), ya musanta alakar da ake zargin ya na da ita da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Ya bayyana hakan ne a wani zantawa d ayayi da jaridar Punch, a inda ya ce sau daya ya taba ganin Dogara shima din daga nesa ne. jam’iyyar APC ta yi wannan zargi ne yayin ta ki amincewa da sakamakon zaben Gwamna na karamar hukumar Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi, a inda Hukumar zaben ta gabatar da sakamakon a mastayin wanda bai kammala ba.

Sai dai kuma, Humkumar zaben ta yi amai ta lashe bisa shawawar da kwamitin bincike ta yi game da abubuwan da su ka faru yayin zaben. Jamiyya mai ci ta ce okoye da dogara abokan juna ne. shi kuwa Dogara ya na marawa dan takarar jam’iyyar PDP baya ne.

KU KARANTA: Majalisar Dinkin Duniya ta ce Talakawa sun fi attajirai kashe kudi wurin samun ruwa

Okoye ya bukaci ‘yan siyasa da su guji yada zantukan da bas u da tushe, ya kuma bayyana cewar a mastayin san a na lawya kuma dan gwagwarmaya, yin hakan ba zai yuwu ma sa ba. Ya kara da cewar, sun yi aiki ne da rahoton da kwamitin bincike ta gabatar ma su.

A baya mun kawo muku rahoton cewa Jam'iyyar APC ta tuhumci kwamitin labaran hukumar INEC da kin bata daman fadin ra'ayinta a matsayin jam'iyyar siyasa kafin soke sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

"Hatta mambobin kwamitin abubuwan zargi ne saboda shugaban kwamiti, Festus Okoye, lauya ne kuma abokin kakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara na jam'iyyar PDP."

"Babu wata adalci da wannan shugaban kwamiti zai iya yi saboda yanada nasa ra'ayin kan abubuwan da yake faruwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel