El-Rufa'i ya kafa kwamitn rantsar da shi

El-Rufa'i ya kafa kwamitn rantsar da shi

A yau, Talata, ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya kaddamar da kwamitin da zai shirya harkokin sake rantsar da shi a matsayin zababben gwamna a karo na biyu wanda za a yi a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya ce kwamitin zai yi waiwaiye don fito da aiyukan da gwamnati ta yi a zangon farko domin ba shi damar fitar taswirar yadda zai tsara aiyukan sa a zango na biyu.

Balarabe Abbas, sakataren gwamnatin jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban kwamitin ya ce za su mayar da hankali wajen bawa bukatun jama'a fifiko kamar yadda gwamnatin jihar ta sha nanata wa.

El-Rufa'i ya kafa kwamitn rantsar da shi
El-Rufa'i da Buhari
Asali: Twitter

Abbas na wannan kalami ne yayin da ya wakilici gwamna El-Rufa'i a wurin rantsar da kwamitin.

DUBA WANNAN: Rundunar ‘yan sanda ta kama jami’anta da su ka gaza tabuka komai yayin kone ofishin INEC

Ya kara da cewa bangarorin da kwamitin zai bawa fifiko sun hada da; yin waiwaye tare da tattara rahoto a kan aiyukan gwamnati daga 2015 zuwa yanzu, fitar da rahoton kwazon ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Ragowar su ne; auna nasarar gwamnati ta fuskar karfin ikon gudanar da aiyuka da kuma tafiyar da harkokin gwamnati, bayar da shawarwari ga gwamnati domin ta san bangarorin da ya kamata ta fi bawa fifiko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel