Za mu kwato maku kuri’unku – Ashiru ya ba mutanen Kaduna tabbaci

Za mu kwato maku kuri’unku – Ashiru ya ba mutanen Kaduna tabbaci

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris da ya gudana, Hon Isa Ashiru Kudan ya ba mutanen jihar tabbacin cewa za a kwato masu kuri’unsu.

Ashiru wanda yace an yi wa mutanen jihar fashin kuri’unsu a zaben gwamna da aka gudanar ya kara da cewa shi da jam’iyyarsa sun kafa tawagar lauyoyi domin tabbatar da cewar an basu hakkinsu a zaben.

Wasu kungiyoyi karkashin jagorancin Farfesa Banake Sambo sun lura cewa ba a yi amfani da na’urar tantance kuri’u ba a wasu mazabu a kananan hukumomi 10 a zaben gwamnan jihar Kaduna da INEC ta kaddamar da gwamna Nasir El-Rufai a matsayin mai nasara.

Za mu kwato maku kuri’unku – Ashiru ya ba mutanen Kaduna tabbaci
Za mu kwato maku kuri’unku – Ashiru ya ba mutanen Kaduna tabbaci
Asali: UGC

Daga cikin kananan hukumomin da aka yi zargin haka sun hada da Giwa, Zaria, Sabon-Gari, Ikara, Lere, Igabi, Soba, kudancin Kaduna da kuma arewacin Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers

Da yake mika sakon godiya ga mutanen jihar Kaduna bayan zaben, Ashiru ya bayyana cewa zai bi hakkin kuri’un da suke nasa a kotu wanda a cewarsa an kwace masa ta hanyar amfani da mulkin jiha.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel