Ku kwana da shirin karin haraji - Hukumar tattara haraji zuwa ga 'yan Najeriya

Ku kwana da shirin karin haraji - Hukumar tattara haraji zuwa ga 'yan Najeriya

Hukumar gwamnatin tarayyar Najeriya dake da alhakin tattara haraji ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) a ranar Talata ta bukaci 'yan Najeriya da su kwana da shirin ko-ta-kwana na karin harin kayayyaki a shekarar nan ta 2019.

Hukumar ta FIRS ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen yin karin harajin na bangaren da ake kira da Value Added Tax (VAT) da kaso 35 zuwa 50 cikin dari domin samar da kudaden shigar da za a iya dabbaka kasafin kudin na 2019.

Ku kwana da shirin karin haraji - Hukumar tattara haraji zuwa ga 'yan Najeriya
Ku kwana da shirin karin haraji - Hukumar tattara haraji zuwa ga 'yan Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda sojoji suka yi biji-biji da 'yan Boko Harama a Michika

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan dai ya fito ne daga bakin shugaban hukumar ta tattara harajin ta kasa watau FIRS mai suna Mista Babatunde Fowler lokacin da yake ansa tambayoyi daga kwamitin majalisar dattawa kan harkokin da suka shafi kudi.

Mista Fowler ya kara da cewa wannan matakin da hukumar da yake shugabanta za ta dauka na daga cikin tsare-tsaren su na ganin sun cimma burin su na tarawa gwamnatin tarayya harajin Naira triliyon 9 a shekarar ta 2019.

A wani labarin kuma, Mista Godwin Emefiele, shugaban babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya bayyana cewa 'yan Najeriya na kashe kudaden da suka kai akalla Dalar Amurka miliyan dari biyar a duk shekara wajen shigo da man ja daga kasashen waje.

Shugaban Central Bank of Nigeria (CBN) din yayi wannan ikirarin ranar Litinin din da ta gabata da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na masu sana'ar man ja a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel