Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers

Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers

Wata babbar kotun tarayya da ked a zama a Abuja ta ba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) umurnin dakatar da tattara sakamako da kuma sanar da sakamakon zaben gwamna da na majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a jihar Rivers.

A cewar Sahara Reporters, Justis Iyang Ewa ya umurci hukumar day a dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben, bisa ga karar da yan takarar jam’ iyyar African Action Congress (AAC) suka shigar.

Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers
Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa mai karan ya roki kotu da tayi umurnin da zai hana INEC ci gaba da tattara sakamako da kuma sanar da sakamakon zaben da aka dage a jihar Rivers.

An rahoto cewa Justis Ewa ya umurci INEC da ta gurfana a gaban kotu a ranar Juma’ a, 22 ga watan Maris, domin sauraron karar da AAC da yan takararta suka shigar.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe

Mai shari’an ya kuma yi zargin tabbatar da cewa kotun za ta bayar da umurninta na karshe bayan ta kammala duba karan da aka shigar gabanta.

Don haka alkalin ya umurci INEC da ta dakatar da tsarin zaben a Rivers har sai kotu ta bayar da umurnin karshe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel