Rundunar ‘yan sanda ta kama jami’anta da su ka gaza tabuka komai yayin kone ofishin INEC

Rundunar ‘yan sanda ta kama jami’anta da su ka gaza tabuka komai yayin kone ofishin INEC

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ebonyi ta sanar da kama wasu jami’anta 6 da suka gaza tabuka komai yayin da wasu batagari su ka banka wa ofishin hukumar zabe wuta yayin da rikici ya barke a zaben gwmna da ‘yan majalisar dokoki.

ASP Loveth Odah, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa a yau, Talata, cewar an kama jami’an ‘yan sandan ne saboda bas u tabuka komai ba a lokacin da batagari ke saka wuta a ofishin na INEC.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar wasu ‘yan daba sun saka wuta a ofishin INEC da ke Umuoghara a karamar hukumar Ezza ta Arewa, lamarin da ya jawo konewar kayan aikin zabe da lalata ginin makarantar da INEC ta yi amfani da ita lokacin zaben.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta ce kamata ya yi jami’an ‘yan sandan su yi yunkurin hana ‘yan dabar saka wuta a ofishin ba su bari matasan su yi abinda su ke so ba.

“Mun yi matukar mamaki yadda jami’an da ya kamata su hana barna su ka kasa tabuka komai yayin da batagarin ke kokarin saka wuta a ofishin INEC.

Ba mu samu labarin sun yi harbi, ko sun raunata wani, ko sun kama wani daga cikin wadanda su ka aikata laifin.

“Rundunar ‘yan sanda ba za ta yarda da lalaci da sakaci da aiki ba, aikin dan sanda shine ya hana barna ba ya bari a aikata barna ba,” a cewar Odah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel