Tsaro: Gwamna Masari ya gana da Osinbajo

Tsaro: Gwamna Masari ya gana da Osinbajo

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce yana ganawa da shugabanin hukumomin tsaro domin gano hanyoyin da za su magance yawan afkuwar satar mutane da hare-haren da 'yan bindiga ke yi a jihar.

Masari ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na gidan gwamnati bayan ganawar sirri da ya yi da mataimakin shugban kasa, Yemi Osinbajo a gidan gwamnati a Abuja.

Ya ce ya kai ziyara gidan gwamnatin ne domin ya taya mataimakin shugaban kasa murnar lashe zabe da zarcewa a kan mulki.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Tsaro: Gwamna Masari ya gana da Osinbajo
Tsaro: Gwamna Masari ya gana da Osinbajo
Asali: Facebook

"Daga cikin matakan da muke dauka a kan garkuwa da mutane da fashi da makami shine na fara ganawa da wasu shugbanin hukumomin tsaro.

"Kafin in bar Abuja, zan sake ganawa da Sufeta Janar na 'yan sanda da kuma shugaban 'yan sandan farar hula DSS.

"Za mu gana ne domin tattauna a kan matakan da muke dauka tare da sojoji da sauran jami'an tsaro da muke aiki da su.

"Abinda mu keyi bai tsaya kawai ga batun karo jami'an tsaro ba akwai batun bullo da sabbin dabarun yaki," inji Gwamnan.

A game da batun zarcewarsa a kan mulki, Masari ya ce aikin da ya yiwa al'ummar jihar Katsina ne dalilin da yasa suka sake zabensa.

Ya ce ya cika alkawurran da ya dauka wa al'ummar jihar Katsina yayin yakin neman zaben 2015 hakan ya sa suka sake zabensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel