Dalilin da yasa na ki cewa komai akan sakamakon zaben 2019 – Obasanjo

Dalilin da yasa na ki cewa komai akan sakamakon zaben 2019 – Obasanjo

- Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilansa na kin cewa komai akan sakamakon zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu

- Obasanjo wanda ya mara wa dan takarar PDP, Atiku Abubakar baya yace yin magana akan lamarin shisshigi ne ga shari'a

- Tuni dai Atiku ya shigar da kara kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben wanda ya bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar da dalilansa na kin tofa komai akan sakamakon zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Obasanjo ya goyi bayan dan takarar Shugaban kasa a jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a zaben wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe.

Dalilin da yasa na ki cewa komai akan sakamakon zaben 2019 – Obasanjo
Dalilin da yasa na ki cewa komai akan sakamakon zaben 2019 – Obasanjo
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Buhari a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’ u 15,191,847 sannan Atiku ya samu kuri’ u 11,262,978.

Sai dai Atiku ya kalubalanci lamarina kotu. Sannan a ranar Litinin, 18 ga watan Maris ne ya maka shugaba Buhari a kotu.

KU KARANTA KUMA: Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya

Obasanjo yace yin Magana akan zaben zai zama yiwa shari’a shisshigi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel