Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya

Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi fatali da wasu kudurorin dokoki guda biyu da majalisar tarayya suka kai masa domin ya sa masu hannu, kamar dai yadda kakakin majalisar wakilan, Yakubu Dogara ya bayyana a zauren majalisar ta wakilai.

Kudurorin da shugaban kasar ya wancakalar din dai sun hada da na kafa wata cibiya da zata rika koyar da hanyoyin lalubo matsaloli da kuma gyaran Najeriya watau Chartered Institute of Training and Development of Nigeria.

Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya
Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya
Asali: UGC

KU KARANTA: Hadarin jirgi: Sanatoci sun yi zaman makokin yan Najeriya

Haka ma dai shugaban kasar ya yi fatali da saka hannu a kan dokar da ta shafi kafa wata manazartar harkokin aikin ceto na sararin samaniya watau Nigerian Aeronautic Research Rescue Bill.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ba wannan ne karon farko ba da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya ki sa wa wani kuduri daga majalisar hannu ba a 'yan kwanakin nan.

A kwanan baya ma dai shugaban kasar ya yi fatali da wani kudurin da yayi gyare-gyare a harkokin zabe.

A wani labarin kuma, Hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu laifuka da suka jibanci damfara watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPS) ta shirya kwace wasu filaye da gine-gine da suka kai darajar Naira biliyan 4.8 daga kamfanoni akalla 30.

Hukumar ta ICPC ta ce za ta kwace kadarorin ne daga hannun masu su saboda karar da aka kai masu na kin biyan harajin da ya kamata su biya na tsawon lokaci kamar dai yadda doka ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel