Sake zabe: Dino Melaye zai jagoranci wata kungiya wajen sanya idanu a gudanarwar zaben

Sake zabe: Dino Melaye zai jagoranci wata kungiya wajen sanya idanu a gudanarwar zaben

Gabannin sake gudanar da zaben gwamna da na majalisar dokokin jiha a wannan makon, hukumar kula da hakkin dan adam na kasa da kasa a Najeriya ta zabi Sanata Dino Melaye don ya jagoranci tawagar masu sanya idanu a zabe.

A wata wasika zuwa ga sanatan, dauke das a hannun Shugaban hukumar a Najeriya da kasashen Afrika, Ambasada Friday Sani, ya bayyana cewa tawagar za su kula da zabe a jihohin Rivers da Kano.

Sake zabe: Dino Melaye zai jagoranci wata kungiya wajen sanya idanu a gudanarwar zaben
Sake zabe: Dino Melaye zai jagoranci wata kungiya wajen sanya idanu a gudanarwar zaben
Asali: Instagram

Wasikar ta bayyana cewa hukumar kare hakkin dan adam na kasa da kasa ta samu shiga cikin masu kula da zaben Najeriya, inda ta bayyana cewa tawagar za su gabatar da rahoton sanya idanu da suka yi bayan kammala zaben.

KU KARANTA KUMA: Tsaffin Jakadu sun nemi a soke maimacin zaben gwamnan jihar Benuwe

Hukumar ta kara da cewa an karfafawa hukumar jan hankali a yayinda ta lura da cewa akwai inda aka saba dokar zaben kasar sannan ta sanar da jama’a.

A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu manyan jagororin APC a jihar Ribas sun bayyana abin da ya faru da su a lokacin da aka sace ana rikita-rikitan zabe.

Wadannan jagorori na APC sun zargi gwamnatin jihar Ribas da kitsa sacen su. Chikordi Dike, da Alex Wele da kuma Lawrence Chuku sun bayyana cewa Yaran Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ne su ka sace su a wurin zabe a cikin Garin Obio Akpor. Dike ya bada labarin yadda abin ya kasance.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel