Dalilin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan wucin gadi ba – INEC

Dalilin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan wucin gadi ba – INEC

Kwamishinan hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar Oyo, Mutiu Agboke, ya alakanta rashin biyan ma’ikatan wucin gadi a zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi da bayar da lambobin asusun banki ba daidai ba da ma’aikatan su ka yi.

Mutiu ya shaidawa jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewar kurakuran da ke cikin lambobin asusun banki da ma’aikatan wucin gadin su ka bayar ne dalilin rashin biyan su kudin aikin su har yanzu.

Ya ce hakan ne ya sa hukumar INEC ta gaza aika kudin aikin zuwa asusun bankunan ma’aikatan da ke hannun su

wasu daga cikin sub a su bayar da lambobin bayanan sun a banki daidai ba. Wasu ma sun bayar da bayanan bankunan wasu daban.

“Yanzu haka mu na kan ganawa domin tattauna yadda za mu warware wannan matsalar domin ganin mun biya kowa kudin sa,” a cewar sa.

Da aka tambaye shi adadin lokacin da zai dauki INEC ta gama warware matsalar, kwamishinan ya ce ba shi da masaniya amma ya kara da cewa za su biya ma’aikatan da zarar sun warware matsalar.

Dalilin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan wucin gadi ba – INEC
Dalilin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan wucin gadi ba – INEC
Asali: Facebook

Kazalika ya ki cewa komai a kan tambaye shi yaushe INEC za ta biya wadanda su ka bayar da bayanan bankin su daidai.

DUBA WANNAN: Abin da likitoci su ka fada bayan ‘yar Najeriya ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin Amurka

Da yawan ma’aikatan wucin gadi daban-daban da su ka bawa INEC gudunmawa wajen gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki a jihohi da dama na cigaba da korafin kin biyan su kudin aikin su duk da irin hatsarin da su ka shiga yayin aikin zaben.

Kokarin majiyar mu na jin ta bakin hedikwatar INEC bai samu ba, saboda rashin samun jami’in hulda da jama’a (PRO), Mista Rotimi Oyekanmi, a kn lambar wayar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel