'Yan bindigan Zamfara suna da makamai da suka fi na sojoji - Gwamna Yari

'Yan bindigan Zamfara suna da makamai da suka fi na sojoji - Gwamna Yari

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce 'yan bindigan da ke kai hare-hare a jihar Zamfara sun fi sojojin da ke yaki da su yawan makamai bayan ganawar da ya yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a gidan gwamnati bayan taron, ya ce baya tsamanin yin sulhu ko afuwa ga 'yan bindigan zai iya kawo karshen hare-haren.

Gwamnan ya ce jami'an gwamnati sun damar duba ma'ajiyan makamai na 'yan bindigan kuma sun gano cewa 'yan bindigan sun mallaki makamai da suka fi na sojojin da ke jihar.

'Yan bindigan Zamfara sun mallaki makamai fiye da sojoji - Gwamna Yari
'Yan bindigan Zamfara sun mallaki makamai fiye da sojoji - Gwamna Yari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

A cewarsa, akwai bindigu kirar AK 47 guda 500 a cikin dakin ajiyar makamai guda daya tak mallakar 'yan bindigan.

Gwamnan ya ce yana kyautata zaton dakarun sojojin za su karya lagwan 'yan bindigan yanzu da makaman da gwamnatin tarayya ta saya na Naira Biliyan 1.

Ya ce, "Tabbas, gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar sayo makamai daga kasahen Amurka da China da kuma sauran kasashen turai.

"Idan ba a manta ba dai kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince da ware Naira Biliyan Daya domin tallafawa gwamnatin tarayya saya wa hukumomin tsaro makamai da suke bukata.

"Muna kyautata zaton da zarar makaman sun iso Najeriya za ayi amfani da su domin magance kallubalen tsaron da muka fama da shi."

A kan yiwuwar yin sulhu da 'yan bindigan, Yari ya ce hakan ba za ta faru a karkashin gwamnatinsa ba saboda ya gwada yin hakan har sau uku amma ba a samu nasara ba. Ya kara da cewa 'yan bindigan suna boya ne a lokacin damina idan daji ya yi kauri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel