Yanzu-yanzu: An janye dokar ta baci a Taraba, an damke mutane 42

Yanzu-yanzu: An janye dokar ta baci a Taraba, an damke mutane 42

Gwamnatin jihar Taraba ta janye dokar ta baci da ta sanya sakamakon rikice-rikicen da ya biyo bayan zaben gwamnan jihar a birnin jihar, Jalingo.

Wannan sako na kunshe ne cikin jawabin da sakataren yada labaran gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, Mallam Hassan Mijinyawa, ya rubuta.

Jawabin ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gamsu da zaman lafiyan da ke cikin Jalingo da sauran sassan jihar a yanzu, saboda haka, ta janye dokar hana fitar da aka sanya tun ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2019.

Hakazalika, kwamandan 22 Army Bataliya, Laftaan Kanal Muhammad Sani Adamu, ya mikawa hukumar yan sandan jihar wasu yan taki zama 42.

Ya ce sun damke wadannan matasa ne a wurare daban-daban cikin Jalingo da kewaye tare da muggan makamai.

KU KARANTA: Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci

A bangare guda, Gwamnatin jihar Taraba karkashin jagorancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana musayar kalamai tsakanin ta da jam'iyyar adawa ta All Progressives Congress (APC) a kan rikicin da ya faru a Jalingo, babban birnin jihar.

Gwamnatin jihar tayi ikirarin cewa magoya bayan jam'iyyar APC ne suka fara kai harin da ya yi sanadiyar barkewar rikicin amma jam'iyyar ta APC sun mayar da martani inda su kayi ikirarin cewa PDP da gwamnatin jihar Taraba ne suka hada kai suka kaiwa magoya bayan jam'iyyar APC hari.

Kwamishin watsa labarai na jihar, Mr Simon Dogari ya yi ikirarin cewa wadanda suka sha kaye a zaben jihar ne suka dauki nauyin 'yan daba domin tayar da rikici a babban birnin jihar a yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel