Gwamna Wike ya tura ‘Yan daba su ka sace mu – Inji Chikordi Dike

Gwamna Wike ya tura ‘Yan daba su ka sace mu – Inji Chikordi Dike

Wasu manyan jagororin APC a jihar Ribas sun bayyana abin da ya faru da su a lokacin da aka sace ana rikita-rikitan zabe. Wadannan jagorori na APC sun zargi gwamnatin jihar Ribas da kitsa sacen su.

Chikordi Dike, da Alex Wele da kuma Lawrence Chuku sun bayyana cewa Yaran Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ne su ka sace su a wurin zabe a cikin Garin Obio Akpor. Dike ya bada labarin yadda abin ya kasance.

Mista Dike yace an jefa su ne cikin wata daga cikin motocin gwamna Nyesom Wike da kimanin karfe 11:00 na dare. ‘Yan APC din su na aiki ne a matsayin wakilan zaben jam’iyyar AAC wanda su ka hada-kai da APC a zaben gwamnan.

KU KARANTA: Rikicin APC ya kai ‘Ya ‘Yan Jam’iyya gaban babban Kotun daukaka kara

Gwamna Wike ya tura ‘Yan daba su ka sace mu – Inji Chikordi Dike
An sace Chikordi Dike da wasu manyan APC ana zaben Ribas
Asali: Depositphotos

Dike ya fadawa ‘yan jarida a cikin Birnin Fatakwal cewa wadanda su ka sace su, sun zo ne da kayan jami’an tsaro masu dauke da taken “Neighborhood Safety Watch” a jikin su. Daga karshe dai INEC ta dakatar da zaben gaba daya.

Sai dai kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Emma Okah, yayi watsi da wannan abu da kusoshin APC su ka fada. Emma Okah yake cewa babu dalilin da zai sa gwamnatin jihar ta sace wasu ‘yan adawan da ba su da wani tasiri.

Gwamnatin Wike ta kuma caccaki ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da ta ce su na yawo da sojoji a cikin gari da nufin murde zaben gwamna da majalisar jiha da aka yi yunkurin yi a wancan lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel